Man City na son sayar da Richards

Micah Richards Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shekara daya ce ta rage a kwantaragin Richards

Kungiyar Manchester City a shirye take ta karbi ko nawa ne kan dan wasan bayanta Micah Richards.

Dan wasan bayan, mai shekaru 26, ya buga wasanni biyu kacal a gasar bara, kuma yanzu haka shekara daya ce ta rage a kwantaraginsa.

Wata majiya da ke kusa da Richards ta ruwaito cewa, babu wata damuwa sosai sai dai ba wani tabbaci na ci gaba da zamansa a Man City.

An haifi Richards a birnin Birmingham na Ingila, ya kuma shiga Man City yana dan shekara 14, sannan ya fara bugawa Ingila wasa a shekarar 2006, yana da shekara 18.

A shekarar 2011 manyan kulobluka sun so sayansa kan kudi fam miliyan 20 amma saboda yawan raunin da ke jikinsa da fitowar Pablo Zabaleta a matsayin zabin City na farko, ya rage damar da ya ke da ita.

Newcastle United da Liverpool da Arsenal su ne ake alakantawa da sayen dan wasan a makonnin da suka gabata, mai yiwu wa yanzu ma su kara nuna sha'awarsu.

Karin bayani