Brazil 2014: Tarihin da aka kafa kawo yanzu

Hakkin mallakar hoto Getty

An bayyyana gasar cin kofin duniya ta Brazil 2014 a matsayin wacce tafi kayatarwa a tarihi kuma akwai alamun da suka tabbatar da haka.

Ana karya tarihin da aka kafa a baya - kamar na zira kwallaye, batun shekarun 'yan wasa da kuma yawan harauffa a suna.

Ga bajinta daban-daban har biyar da suka fi yin fice da aka kafa a Brazil 2014.

Sada zumunta

Wannan gasa ta kafa tarihi a shafukan sada zumunta inda shafukan Facebook da Twitter suka samu adadi mafi yawa na mutanen da ke tattaunawa kan gasar.

An aika sakonnin Twitter miliyan 16 da rabi a lokacin da Brazil ta doke Chile a bugun fenareti, ciki har da sakonni 388,985 a karshen wasan - wanda ya sa ya zamo abinda aka fi aika sakonni a kansa a tarihin shafukan sada zumunta.

Hakkin mallakar hoto Getty

Mutane biliyan daya ne suka rinka magana a lokacin gasar a Facebook - adadi mafi girma a tarihin shafin, cikin shekaru 10 da kafuwa.

Kwallaye

A wannan gasar ce aka fi zura kwallaye fiye da kowacce a tarihi, inda aka zira kwallaye 136 a wasannin rukuni.

Kuma hakan ya ci gaba, inda kwallon da Paul Pogba na Faransa ya zura wa Nigeria ta zamo ta 146 - abinda ya zarta adadin da aka zura baki daya a gasar da ta gabata a Afrika ta Kudu da kwallo daya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mondragon ya shige gaban Milla

Colombia na taka rawar gani sosai inda ta lashe wasanni hudun da ta buga kawo yanzu a karon farko a tarihinta, sannan ta kai zagayen dab da na kusa da na karshe.

Kuma a yanzu suna da dan wasa mafi tsufa da ya taka leda a gasar, bayan da golansu mai shekaru 43 Faryd Mondragon ya zarta tarihin da dan Kamaru Roger Milla ya kafa a shekarar 1990 lokacin yana da shekaru 42.

Daga Papastathopoulos zuwa Jo

Duk da cewa an fitar da kasar Girka, sun bar Brazil tare da dan wasansu ya zamo wanda ya fi dogon suna a jeren 'yan wasan da suka zura kwallo a tarihin gasar.

Hakkin mallakar hoto AFP

Sokratis Papastathopoulos ya kafa tarihin ne bayan da ya zura kwallon da ta baiwa Girka damar farke kwallon da Costa Rica ta zura mata.

Shi ma dan wasan Brazil Jo ya zamo dan wasa mafi karancin suna da ya taka leda a gasar cin kofin duniya.

Gyan - Gwarzo a Afrika

Ghana ba ta taka rawar gani a gasar ba, amma kuma dan wasan Black Stars din, Asamoah Gyan ya zamo dan Afrika da ya fi kowa zura kwallo a tarihin gasar.

Hakkin mallakar hoto AFP

Kwallon da Gyan ya zura a wasa tsakanin Ghana da Portugal, ta sa adadin kwallayen da ya zura sun kai shida.

Dan wasan mai shekaru 28 ya kuma yazo dan Afrika na farko da ya zura kwallaye a gasar cin kofin duniya uku daban-daban.

Karin bayani