Algeria za su tallafa wa Palasdinawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan ne karon farko da Algeria suka kai zagaye na biyu

'Yan wasan Algeria za su bayar da kudaden da suka samu daga gasar cin kofin duniya ga al'ummar Palasdinu da ke zirin Gaza.

Jamus ce ta fitar da Algeria a zagaye na biyu na gasar, amma dan wasan gaba Islam Slimani ya tabbatar da kyautar da shi da abokan wasansa suka yi.

Slimani, wanda ke taka leda a Sporting Lisbon ya kara da cewa "suna bukatar kudin fiye da mu".

Sabanin takwarorinsu na Kamaru da Ghana da Nigeria da suka rinka rigima kan kudaden da za a biya su, 'yan Algeria halin dattaku suka nuna.

Algeria sun koma gida cikin kyakkyawar tarba ranar Laraba inda dubban jama'a suka fita kan tituna domin tarbarsu.

Karin bayani