Liverpool sun dauki Emre Can

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emre Can na taka leda sosai a Bayer Leverkusen

Liverpool sun kammala sayen dan wasan Jamus na 'yan kasa da shekaru 21 Emre Can daga kungiyar Bayer Leverkusen.

Kulob din ya amince ya biya fam miliyan goma kan dan wasan mai shekarr 20 a watan da ya gabata, amma sai da suka jira aka bude kakar musayar 'yan wasa a farkon watan Juli sannan aka kammala cinikin.

"Emre matashin dan wasa ne kwararre kuma na yi farin ciki da ya zabi Liverpool," a cewar kocin kulob din Brendan Rodgers.

Can shi ne dan wasa na uku da Liverpool suka dauka a bana, bayan zuwan 'yan Southampton Rickie Lambert da Adam Lallana.

Karin bayani