'Pogba zai zama gwarzon dan wasa'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pogba yana taka leda sosai a Juventus da Faransa

Rio Ferdinand ya ce matashin dan wasan tsakiyar Faransa Paul Pogba na cikin taurarin gasar cin kofin duniya, sai dai rawar da ya taka ba ta bada mamaki ba.

"Pogba bai yi wasanni da yawa ba lokacin yana Manchester United amma abubuwan da ya yi a wajen karbar horo ya tabbatarwa da dukkan 'yan wasan United cewa yana da kyau." In ji Rio Ferdinand.

Ya kuma kara da cewa, "Hakika ba karamin abin takaici ba ne komawarsa Juventus a shekarar 2012, haka kuma Man United ta yi kuskure da ta sake shi."

Ferdinand na ganin dan wasan mai shekaru 21, "ka iya zama dan kwallon tsakiyar da ya fi kowanne iya taka leda".

Karin bayani