Brazil ta kai wasan kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Thiago Silva da David Luiz ne suka ci wa Brazil kwallayenta biyu, kafin Colombian ta ci daya da bugun fanareti.

Brazil ta kai wasan kusa da karshe na gasar cin kofin duniya da take karbar bakunci bayan ta doke Colombia da ci 2-1.

Sai dai kuma Brazil din ta yi asarar dan wasan da yafi zura mata kwallaye a gasar, Neymar saboda raunin da ya ji a kashin bayansa.

Raunin ya sa ba zai iya ci gaba da wasa a gasar ba.

'Yan wasan baya na Brazil din Thiago Silva da David Luiz ne suka ci mata kwallayenta biyu, kafin daga bisani Colombian ita ma ta ci daya a bugun fanareti.

Kafin bayyana labarin raunin Neymar din, masu sha'awar wasan kwallon kafa 'yan kasar ta Brazil, har sun fara bidire da birede, inda aka fara baje kolin kade kaden Samba, a Sao Paulo da kuma wasan wuta a wurin shakatawa na bakin teku na Copacabana.

A wasan kusa da karshe da Brazil za ta yi da Jamus wadda kafin wasan na Brazil a jiya ta fitar da Faransa da ci 1-0, kyaftin din Brazil Thiago Silva ba zai buga ba, saboda alkalin wasa ya sallame shi a karawar da Colombia.

Karin bayani