Djokovic da Federer sun kai wasan karshe

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ne karo na tara da Federer ke kaiwa wasan karshe

Novak Djokovic zai kara da Roger Federer a wasan karshe na gasar Tennis ta Wimbledon bayan duka 'yan wasan biyu sun yi nasara a wasanninsu.

Djokovic ya tsallake ne bayan ya doke Grigor Dimitrov a zagaye hudu.

Dan wasan na Serbia ya lashe wasan ne da ci 6-4 3-6 7-6 (7-2) 7-6 (9-7), sai dai duka 'yan wasan biyu sun ji jiki.

Shi kuwa Federer ya samu damar kaiwa wasan karshen ne a karo na tara bayan ya doke Milos Raonic da ci 6-4 6-4 6-4.

Wannan ne karo na uku da Djokovic ke kaiwa wasan karshe a shekaru hudu.

Karin bayani