'Yan wasan Jamus na fama da rauni

Joachim Low Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jamus ta kammala wasanninta a rukunin G inda ta yi nasara a 2 ta kuma yi canjaras a daya

Kociyan Jamus Joachim Low ya ce yana fatan zakulo fitattun 'yan wasa da za su buga a karawar da Jamus din za ta yi da Faransa a ranar Juma'a.

Mr Low ya ce, ya na da kwarin gwiwar cewa 'yan wasan da ke fama da jinya za su murmure har ma su taka leda a wannan wasa na dab da na kusa da na karshe.

Sai dai har yanzu ba a fitar da sunayen 'yan wasan 7 da ke da larura ba, amma a wannan makon dan wasan baya Mats Hummels da dan wasan tsakiya Christoph Kramer sun yi fama da rashin lafiya.

Haka kuma 'yan wasan ba su buga wasan da Jamus din ta yi da Algeria ba, inda ta samu nasara da ci 2-1.

Jamus wacce ta dauki kofin duniyar har sau 3, na fatan ganin ta sa ke kaiwa ga wasan kusa da na karshe a karo na 4 a Gasar cin kofin duniya.