Nigeria za ta fuskanci fushin Fifa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ta halarci gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, za ta iya dakatar da Nigeria daga harkokin kwallon kafa saboda tsoma bakin gwamnati a hukumar kwallon kafa ta kasar.

Gwamnatin Nigeria ta nada shugaba na riko domin ya jagoranci hukumar kwallon kafa ta (NFF) ranar Alhamis, bayan da kotu ta kori shugabannin hukumar.

A karkashin dokokin Fifa, wajibi ne hukumomin kwallon kafa na kasashe su kasance masu cin gashin kansu ba tare da sa hannun gwamnati ba.

A shekara ta 2010 Fifa ta yi barazanar dakatar da kasar bayan da gwamnati ta tsoma baki.

A ranar Alhamis, ministan wasannin Nigeria Tammy Danagogo, ya nada Lawrence Longyir Katiken, domin ya jagoranci hukumar ta NFF.

Matakin ya zo ne bayan da kotu a birnin Jos ta bayar da 'hukuncin wucin gadi' na dakatar da shugaban NFF Aminu Maigari da kuma kwamitin gudanarwarsa.

Karin bayani