Traore ya sabunta kwantiragi da QPR

Armand Traore Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Armand Traore na fatan taka rawar gani a QPR

Armand Traore ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragin shekaru biyu da kungiyar Queens Park Rangers.

Dan wasan bayan na Senegal ya sanya karin kwantiragin ne wacce za ta zaunar da shi a kulob din har shekara ta 2016.

"Sabuwar kakar wasa ta bana na da muhimmanci a gare ni, ga shi kuma mun dawo gasar Premier," a cewar Traore.

"Ina so na nuna irin rawar da zan iya taka wa a gasar League da ta fi kowacce a duniya.

Shekaru na 24 yanzu - a don haka lokaci ne da zan zage damtse domin cimma wani abu."