Valencia ta nada Nuno a matsayin koci

Nuno Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nuno ya dade yana taka leda a Spain da Portugal

Kungiyar kwallon kafa ta Valencia ta nada tsohon mai tsaron gidan Porto da Deportivo La Coruna Nuno a matsayin sabon koci.

Nuno mai shekaru 40, wanda shi ne mai kula da kolub din Rio Ave tun shekarar 2012, za a tabbatar da shi a matsayin sabon kocin ranar Juma'a.

Kolub din ya ce sun cimma yarjejeniya da Nuno Espirito Santo kan kwantiragi wadda za ta kare a ranar 30 ga watan Yunin 2015, tare da zarafin tsawaita wa.

Nuno, zai karbi kulob din daga hannun Antonio Pizzi wanda aka sallama a wannan makon, watanni shida kacal da fara aiki.

Sabon kocin ya bar Deportivo a shekarar 2002 bayan ya kwashe shekaru biyar, ya kuma koma Porto inda ya ci kofin gasar zakarun Turai karkashin jagorancin Jose Mourinho.