Argentina ta kai wasan kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An zira wa Belgium kwallaye uku ne kawai a wasanninsu biyar na gasar ta Brazil

Argentina ta kai wasan kusa da karshe na kofin duniya a karon farko tun lokacin da ta zo ta biyu a 1990, bayan ta doke Belgium da ci 1-0.

Gonzalo Higuain ne ya ci kwallon a minti takwas na wasan, da hakan ya kawo karshen wasanni shida da yake buga wa kasarsa ba tare da ya ci kwallo ba.

Kwallon ta sa Higuain ya kamo Messi a yawan kwallaye biyar da ya ci wa Argentina a gasar kofin duniya, inda ya yi wasanni tara, Messi kuma ya yi 13.

A wannan wasan Lionel Messi ya kamo tsohon gwarzon dan wasan Argentinan Diego Maradon na yi wa kasar wasanni 91.

Wannan shi ne karon farko a tarihin kofin duniya da Argentina da Brazil suka kai wasan kusa da karshe tare.

Karin bayani