Holland ta kai wasan kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Holland ta mamaye wasan, amma daga karshe Costa Rica ta farfado

Holland za ta kara a wasan kusa da karshe na kofin duniya da Argentina bayan da ta fitar da Costa Rica a bugun fanareti 4-3.

Bayan kammala minti 90 na wasan da kuma karin lokacin fitar da gwani na mintina 30 ba kasar da ta ci, shi ne a ka yi fanareti.

Golan Holland Tim Krul wanda ya shigo a karin lokacin minti 30 shi ne ya buge fanareti biyu ta 'yan Costa Rica; Bryan Ruiz da Micheal Umana.

A lokacin wasan sau biyu Wesley Sneijder yana buga kwallo tana dukan tirken raga, shi ma Robin van Persie ya buga wata ta bigi karfen saman raga.

Kafin karawar ta Holland da Costa Rica, Argentina ta fitar da Belgium da ci 1-0.

Karin bayani