Messi ya ceto Argentina

Messi ya yi namijin kokari Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Messi na murnar nasarar Argentina

Mai bada horo na Argentina ya ce Kaftin din Argentina Lionel Messi ya ceto kasar a gasar cin kofin duniya yayin da take ta fadi tashi.

Messi ya jagoranci tawagar zuwa wasan kusa da na karshe tun shekarar 1990 yayin da Gonzalo Higuan ya doke Belgium.

Mai bada horon ya ce " dan wasa kamar Messi wanda baya rasa doka wasa mai kyau tamkar ruwa ne a dokar daji."

Dan wasan mai shekaru 27 gwarzon Barcelona ya yi sanadiyyar zura kwallo daya wanda ya basu nasara kan Belgium.

Karin bayani