Mafarkin Neymar bai gushe ba

Neymar bai fidda raiba da zama zakara Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Neymar an dauke shi a jirgi mai saukar ungulu zuwa asibiti

Dan wasan kasar Brazil din nan dan gaba Neymar ya ce mafarkin da ya ke yi na zama zakaran duniya bai gushe ba duk kuwa da cewa ba zai buga shauran wasannin ba saboda ciwon baya.

Dan wasan mai shekaru 22 ya sami karaya a kashin bayansa bayan da Juan Zuniga ya buga masa gwiwa a baya a wasan da Brazil ta ci Colombia 2-1.

Dan wasan Barcelona ya ce mafarkin na sa ya fauskanci cikas amma fa yana ci gaba.

Nasarar da masu ma saukin bakin su ka samu kan Colombia ta sa za su kara da kasar Jamus.

Karin bayani