Dejan zai koma Liverpool

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dejan Lovren na jin kanshin komawa Liverpool

A farkon wannan mako ne , Dejan mai shekaru 25 ya shaidawa kafofin watsa labarai na Crotia cewa zai koma Liverpool inda zai samu fan miliyan 20.

Duk da cewa ba a daddale cinikin ba, Lovren ya ce tuni ya na jin kanshin kungiyar ta Liverpool.

Tuni dai ake ganin cewa Rickie Lambert, da Adam Lallana da Luke Shaw da kuma manaja Mauricio Pochettino za su bar kungiyar a wannan bazarar.

A yanzu haka dai Rikie Lambert da kuma Adam Lallana sun koma Liverpool a cikin bazara shi kuma Luke Shaw ya koma Manchester United.

Karin bayani