Ashley Cole zai koma AS Roma

 Ashley Cole Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ashley Cole ya shafe shekaru 11 a Chelsea

Ana sa ran tsohon dan wasan Chelsea Ashley Cole zai koma kulob din AS Roma a ranar Litinin, kamar yadda wakilinsa ya tabbatar.

Kulob din na Serie A a Italiya, sun wallafa sakon lale-marhabin ga dan wasan a shafinsu na Twitter tare da hotonsa lokacin da yake isa birnin Rome.

Wakilin Cole, Jonathan Barnett, ya ce: "Ashley yana Italiya kuma muna sa ran kammala komai a yau."

Dan wasan ba shi da kulob a yanzu bayan da Chelsea ta ki sabunta kwantiraginsa a karshen kakar wasannin da ta kare.

BBC ta fahimci cewa tsawon kwantiragin da zai sa hannu na daga cikin abubuwan da suka rage a cimma matsaya a kai.

Karin bayani