Wasan Holland ban da Di Maria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Watakila Angel Di Maria ya buga wasan karshe

Dan wasan gefe na Argentina, Angel Di Maria ba zai buga a karawar kusa da karshe ta cin kofin duniya da Holland ba a ranar Laraba, amma Sergio Aguero na da koshin lafiyar taka leda.

Di Maria, dan shekaru 26, ya ji ciwo ne a wasan daf da kusa da na karshe yayin karawa da Belgium.

Dan wasan na kulob din Real Madrid, wanda aka duba lafiyarsa ranar Lahadi, ya samu cirar tsoka a cinyarsa don haka ba zai buga wasa da Hollande ba.

Sai dai, Aguero, mai shekaru 26, ya koma atisaye kuma yana da koshin lafiyar bugawa a karawa ta gaba bayan ya rauninsa a wasan Argentina da Nigeria.

Di Maria, wanda ya jefa kwallo bayan karin lokaci a wasan da Argentina ta doke Switzerland don kai wa ga zagaye na gaba, ka iya samun sauki don buga wasan karshe a ranar Lahadi.