Origi da Markovic za su koma Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Origi ya haskaka a gasar cin kofin duniya

Liverpool ta amince tsakaninta da kungiyar Lille don sayen dan kwallon Belgium, Divock Origi sannan kuma ta yi nisa a tattaunawar sayen Lazar Markovic daga Benfica.

Liverpool za ta biya fan miliyan 10 kan Origi mai shekaru 19, kuma a wannan makon dan wasan zai tattauna don kammala cinikin.

Sannan ana saran kungiyar ta kammala cinikin Markovic mai shekaru 20 a kan fan miliyan 25.

Wannan yinkurin na daga cikin shirye-shiryen Liverpool na cefanar da Luis Suarez zuwa Barcelona a kan fan miliyan 75.

Har ila yau, Liverpool na sauraron shawarar da Alexis Sanchez zai yanke game da koma wa Anfield a yayinda Arsenal da Juventus ke zawarcinsa.

Karin bayani