Alfredo Di Stefano ya rasu

di_stefano Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Di Stefano ya kafa babban tarihi a fagen kwallon kafa

Shahararren tsohon dan wasan Real Madrid Alfredo Di Stefano, wanda ake kallon yana daya daga cikin 'yan wasan da suka fi kowanne a tarihin tamola, ya rasu.

Dan shekaru 88 ya gamu da bugun zuciya ranar Asabar sannan aka kwantar da shi a asibitin Gregorio Maranon da ke Madrid.

Real Madrid sun tabbatar da labarin, suna masu cewa Di Stefano, wanda shi ne shugabansu na jeka-na-yika, ya mutu da misalin karfe 5.15 agogon Spain.

Ya lashe kofin zakarun Turai sau biyar ajere, inda ya zira kwallo a duka wasannin karshe tsakanin 1956 da 1960.

Shugaban Real Florentino Perez, ya ce shi da kulob din na 'nuna alhininsu da kauna ga 'ya'ya da iyalai da 'yan uwan marigayin'.