'Rashin Neymar ba zai kawo cikas ba'

Kociyan Brazil Scolari da Neymar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Neymar ya ci kwallaye 4 cikin kwallaye 10 da Brazil ta ci a gasar

Kocin Brazil Luiz Felipe ya ce 'yan wasan kasar zasu bada mamaki a karawar su da Jamus duk kuwa da rashin shahararren dan wasan gaban su Neymar.

Dan wasan mai shekaru 22 ya samu karaya ne a kafarsa a lokacin wasansu da Columbia inda suka tashi wasan 2-1.

Shi dai Neymar ya ci kwallaye 4 cikin kwallaye 10 da Brazil ta ci kuma ba zai sake wasa ba a gasar sakamakon karayar da ya ke fama da ita.

Scolari ya ce tawagarsa a shirye take don tunkarar wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin duniya inda ya ce, "Neymar ya yi nasa kokarin, kuma yanzu ya rage namu mu yi abin da ya kamata."