Man City ta sayi Caballero daga Malaga

Willy Caballero Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man City na kokarin kare kanbunta na Premier

Manchester City ta kammala cinikin golan Malaga Willy Caballero a kan kudi fam miliyan shida.

Dan wasan na Argentina, mai shekaru 32, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku.

Caballero, wanda ya taka leda a karkashin kocin City Manuel Pellegrini a Malaga, ya je birnin Manchester ranar Litinin domin kammala jarjejeniyar.

Shi ne dan wasa na uku da City ta saya bayan Fernando daga Porto da kuma tsohon dan wasan Arsenal Bacary Sagna.

Karin bayani