Babu Farah a tseren Diamond League

Mo Farah Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mo Farah na fatan haskaka wa a gasar Commonwealth

Zakaran tseren duniya da Olympic Mo Farah ya janye daga gasar tseren Diamond League a Glasgow saboda rashin lafiya.

An kwantar da dan tseren mai shekaru 31 a wani asibiti a Amurka saboda baya jin dadi a makon da ya gabata.

A ranakun 11-12 ga watan Yuli ne za a yi gasar ta Glasgow.

Farah, wanda aka tsara zai yi tseren mil biyu a Hampden Park, za a sake yi masa gwaji a Burtaniya a wannan makon.

Sai dai yana fatan samun nasara domin ya shiga gasar wasanni ta Commonwealth da za a yi nan gaba a wannan watan a birnin na Glasgow.