Nijeriya za ta iya fuskantar fushin FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

Ranar talata ne wa'adin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta baiwa Nijeriya na mayar da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar watau Aminu Maigari kan mukaminsa ke cika.

A makon da ya gabata ne Ministan harkokin wasanni na kasar Dr. Tammy Danagogo ya sanar da rusa hukumar kwallon kafa ta kasar karkashin jagorancin Aminu Maigari inda ya maye gurbinsa da Lawrence Longyir Katiken a matsayin shugaban hukumar na riko.

Sai dai hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta yi tir da wannan mataki inda ta bukaci hukumomin Nijeriya da su gaggauta maida shugabannin hukumar kwallon kafa ta kasar da aka kora daga kan mukamansu.

FIFA dai na iya haramtawa Nijeriya shiga duk wasu wasanni na duniya matukar kasar ta ki bin umurnin ta.

Karin bayani