Jamus ta lallasa Brazil da ci 7-1

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption David Luis da sauran 'yan wasa sun taka mummunar rawa

Jamus ta fitar da masu masaukin baki Brazil bayan da suka yi musu dukan kawo-wuka da ci 7-1, abinda ya basu damar kaiwa wasan karshe.

Kwallo hudu Jamus suka zira a mintina shida -Thomas Muller ne ya fara zira ta farko.

Kafin Miroslav Klose ya ci ta biyu - inda ya zamo dan wasan da ya fi kowa zira kwallo a tarihin gasar da kwallaye 16.

Toni Kroos ya zira ta uku da ta hudu kafin Sami Khedira ya ci ta biyar daga yadi na 12.

Andre Schurrle ya kara kwallo biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci kafin Oscar ya ciwa Brazil kwallo dayan da suka samu.

Jamus za su kara da Argentina ko Netherlands - wadanda za su kara da juna a ranar Laraba - a wasan karshe ranar Lahadi.

Karin bayani