Scolari: 'Ranar takaici ce a gare ni'

'Yan wasan Brazil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Brazil

Kocin tawagar 'yan wasan Brazil Luiz Felipe Scolari ya bayyana shan kashin da Brazil din ta yi inda Jamus ta lallasa ta da ci 7-1 a matsayain ranar mafi muni a rayuwarsa inda ya dora alhakin al'amarin a kansa.

An dai zurawa Brazil mai daukar bakunci gasar kwallaye 5-0 tun kafin a tafi hutun rabin lokaci a filin wasa na Belo Horizonte inda Jamus ta kai ga zagayen karshe a gasar cin kofin duniya.

Scolari, wanda ya jagoranci tawagar a gasar shekara 2002, ya ce zai ci gaba da tuna wannan rashin nasara da suka fuskanta na ci 7-1, amma dama yana sane da yiwuwar fuskanta irin wannan takaici lokacin da na karbi wannan aiki.

Yace, "Ni ne na tsara yadda za a gudanar da wasan, hikimomin tafiyar da wasan, duk wannan tsari na ne."

Scolari ya bayyana sakamakon wanda ya zarta wasansu na karshe a gasar cin kofin duniya da Faransa inda ta sha kashi da ci 3-0 a matsayin 'Iftila'i'.

Tsohon kocin kulob din Chelsea, ya mika sakonsa ga 'yan Brazil inda ya nemi a yi musu uzuri bisa wannan sakamako.

Karin bayani