Juventus na neman Patrice Evra

Patrice Evra Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Patrice Evra ya buga wasanni 379 a Man United

Juventus sun tuntubi Manchester United kan yiwuwar sayen dan bayan Faransa Patrice Evra.

Jami'an kulob din na Italiya sun yi magana da jami'ai a Old Trafford - duk da cewa ba a gabatar da bukatar sayen dan wasan mai shekaru 33 ba kawo yanzu.

A kwanakin baya ne dan wasan ya tsawaita kwantiraginsa da shekara daya a United.

Evra ya buga wasanni 45 a Man United a kakar wasannin da ta gabata inda suka kare a mataki na bakwai.

Tuni dai United ta dauki matashin dan wasan Ingila Luke Shaw, wanda ake ganin zai iya maye gurbin Evra idan har aka sayar da shi.