'Yan Holland 'sun ji tsoron fanareti'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An tashi wasa babu ci bayan shafe mintina 120

Kocin Netherlands Louis van Gaal ya ce biyu daga cikin 'yan wasansa sun ki yadda su buga fanaretin farko a wasan da Argentina ta fitar da su.

Dan wasan baya Ron Vlaar ne ya buga fanaretin farko sai dai Sergio Romero - golan Argentina, wanda Van Gaal ya koya wa yadda ake kade fanareti a kulob din AZ Alkmaar - ya kade kwallon.

Argentina ta lashe bugun fanaretin da ci 4-2 inda a yanzu za ta kara da Jamus a wasan karshe a ranar Lahadi.

"Na nemi 'yan wasa biyu su dauki fanaretin farko kafin na yanke shawara kan Vlaar," a cewar sabon kocin Manchester United Van Gaal.

An tafi bugun fanareti ne bayan an shafe mintina 120 babu ci a tsakanin kasashen biyu.

Karin bayani