Ivory Coast na neman sabon koci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ivory Coast sun kasa kaiwa zagaye na biyu a gasar ta Brazil

Hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast ta nemi masu sha'awa suka gabatar da bukatunsu domin neman zamowa sabon kocin kasar.

A makon da ya gabata ne dan Italiya Giovanni Trapattoni ya shaida wa wani gidan rediyon Itlaiya cewa yana tattaunawa domin zama kocin kasar.

Sai dai hukumar ta ce za ta karbi bukatun masu neman mukamin har zuwa ranar 14 ga watan Juli.

Ivory Coast na neman sabon koci ne bayan tafiyar Sabri Lamouchi, wanda kwantiraginsa ta kare a karshen wasannin da kasar ta buga a gasar cin kofin duniya.

Lamouchi ya kasa kai kasar ga zagaye na biyu na gasar ta Brazil 2014.

Karin bayani