Mourinho ya kare David Luiz

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption David Luiz shi ne kyaftin din Brazil a wasan

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce bai kamata a rinka dora laifin fitar da Brazil daga gasar kofin duniya kan David Luiz shi kadai ba.

David Luiz a Chelsea ya ke taka leda kafin ya koma PSG a karshen kakar wasannin da ta kare.

Mourinho, wanda shi ne jakadan musamman kan kwallon kafa na Yahoo, ya shaida wa Yahoo Sport cewa kowa na da laifi a tawagar ta Brazil.

"Babu adalci a ware dan wasa daya daga cikin tawaga, saboda gaba dayansu basu yi kokari ba. Babu shakka David ya yi kuskure.

"Sai dai, Dante ma ya yi kuskure, Marcelo, Fernandinho duka sun yi kuskure. Gaba daya tawagar shirme suka buga."

Karin bayani