Nigeria na kamun kafa ga FIFA

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nigeria ta kai zagaye na biyu a gasar kofin duniya ta 2014

Jami'an Nigeria sun isa Brazil domin tattaunawa da hukumar kwallon kafa ta Fifa a kokarin da ta ke na kaucewa dakatarwa daga kwallon kafa.

Tsohon mamba a kwamitin zartarwa na Fifa Amos Adamu na cikin tawagar ta Nigeria.

Fifa, wacce ke adawa da tsoma bakin gwamnati a harkar kwallo, ta baiwa Nigeria zuwa ranar Talata ta mayar da shugabannin hukumar NFF da aka kora.

A makon da ya gabata ne aka kori shugabannin hukumar kula da kwallon kafa ta NFF, sannan aka maye gurbinsu da na riko.

Nigeria ta ce matakin ya zama wajibi saboda shari'ar da ake yi kan shugabannin hukumar.

Gwamnatin ta kuma ce an tura takardun da ke nuna cewa matakin da aka dauka ya yi daidai da dokokin Fifa, a don haka ya kamata a amince da matakin.

Karin bayani