Wanne zabi ne ya rage wa Nigeria?

Image caption Aminu Maigari ya musanta zargin da ake yi masa

Nigeria na da zabi daya ne kacal kan dakatarwar da hukumar kwallon duniya Fifa ta yi mata daga shiga harkokin kwallon kafa na duniya, a cewar masana.

Alhaji Shehu Malami, mai sharhi kan harkokin kwallon kafa a kasar, ya shaida wa BBC cewa wajibi ne hukumomi su mayar da shugabancin hukumar kwallon kasar ta NFF ga Aminu Maigari.

"Akwai wasanni da ke gabatowa kamar gasar cin kofin duniya ta mata 'yan shekaru 20, da gasar maza ta 'yan shekaru 17, da wasannin neman shiga gasar cin kofin kasashen Afrika".

A makon da ya gabata ne aka kori shugabannin hukumar kula da kwallon kafa ta NFF, sannan aka maye gurbinsu da na riko.

15 ga watan Yuli

A don haka wajibi ne Nigeria ta yi wani abu idan har tana son a ci gaba da damawa da ita a fagen tamola, a cewar Alhaji Shehu.

Fifa, wacce ke adawa da tsoma bakin gwamnati a harkar kwallo, ta baiwa Nigeria zuwa ranar Talata ta mayar da shugabannin hukumar NFF da aka kora.

Rahotanni sun ce an kama shugaban NFF Aminu Maigari, bayan da ya koma Nigeria daga Brazil bisa zargin aikata ba daidai ba.

Fifa ta sanya ranar 15 ga watan Yuli domin a shawo kan lamarin ko a hana tawagar 'yan kasa da shekaru 20 ta Nigeria shiga gasar cin kofin duniya ta mata.

Karin bayani