Fifa ta yi watsi da bukatar Suarez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Suarez ya nemi afuwar Chiellini

Hukumar kwallon kafa ta duniya- Fifa ta yi watsi da bukatar dan kwallon Uruguay, Luis Suarez bisa daukaka karar da ya yi kan batun dakatar da shi na watanni hudu saboda cizon, dan Italiya Giorgio Chiellini.

Fifa ta kuma haramta mashi buga wa kasar sa wasanni tara nan gaba.

Hukumar kwallon Uruguay ta ce hukuncin Fifa "ya yi tsauri" saboda "babu cikakkiyar hujja".

Suarez na da damar daukaka kara zuwa kotun hukunta manya laifuka ta duniya watau CAS.

Lokacin da lamarin ya faru, Suarez ya nemi afuwar Chiellini a yayinda Fifa kuma ta ci tararsa fan dubu 65.