Arsenal na gab da sayen Sanchez

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alexis Sanchez ya haskaka tare da Chile a Brazil

Kungiyar Arsenal na dab da kammala yarjejeniyar sayen dan wasan gaban Barcelona, Alexis Sanchez.

Arsenal ta cimma yarjejeniya ciniki kan ka'ida, sannan dan wasan mai shekaru 25 ya amince da wasu sharudda tsakaninsa da Arsenal.

Kungiyar ta Arsenal za ta biya fam miliyan 30 kan dan wasan dan kasar Chile wanda ya koma Barca daga Udinese a shekarar 2011, ya kuma ci kwallaye 43 a wasanni 119 da ya buga.

Haka kuma Arsenal na kan hanyar ta na daukar Mathieu Debuchy daga Newcastle United.

Sai dai har yanzu akwai abubuwa da za a kara yin nazari kansu kafin Sanchez ya koma Arsenal.