Ina nan daram tare da Brazil - Scolari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bayan da Jamus ta lallasa Brazil

Luiz Felipe Scolari ya ce ba zai yanke shawara ba game da matsayinsa na kocin tawagar Brazil, har sai bayan kamalla gasar cin kofin duniya.

Scolari mai shekaru 65, na fuskantar suka daga kafafen yada labarai a Brazil inda suka bukaci ya ajiye aiki sakamakon lallasawar da Jamus ta yi musu da ci 7 da 1.

Amma ya hakikance ba zai ce komai ba har sai bayan wasansu na ranar Asabar tsakaninsu da Netherlands don neman gurbi na uku a gasar.

Scolari yace "Har yanzu aikinmu bai kare ba, har sai bayan kamalla gasar cin kofin duniya."

Scolari wanda ya jagoranci Brazil ta lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2002, ya kara dawowa a matsayin kocin tawagar a watan Disambar 2012.