Brazil: An tsaurara tsaro a Rio

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen ruwa 25 ne za su yi gadin gabar ruwan birnin na Rio de Janeiro

Wani babban jami'in gwamnatin Brazil ya ce, birnin Rio de Janeiro na haramar ganin aikin tsaron da ba a taba yi ba a tarihin birnin, domin wasan karshe na cin kofin duniya na kwallon kafa da za a yi tsakanin Argentina da Jamus, ranar Lahadi.

Sama da 'yan sanda da 'yan kwana-kwana da sauran jami'an tsaro dubu 25 ne za su yi aikin tabbatar da tsaron.

Jose Mariano Beltrame, ya ce, ''muna bukatar ganin wannan wasan ya gudana kamar yadda sauran suka kasance.

A kwai yuwuwar yin zanga zanga, kuma gashi birni ne babba da ke bukatar kulawar mu.''

Ana sa ran shugabar kasar, Dilma Roussef, za ta halarci wasan na karshe a filin wasa na Maracana tare da wasu shugabannin kasashe akalla tara, da suka hada da shugaban Rasha Vladimir Putin da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel.

Jiragen ruwa 25 ne kuma za su yi gadin gabar ruwan birnin na Rio, yayin da za a fara wasa tsakanin Brazil da Holland ranar Asabar domin neman kasa ta uku.