Chamakh ya sabunta kwantiragi a Palace

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chamakh ya shafe shekara daya a Palace daga Arsenal

Dan kasar Morocco Marouane Chamakh ya sanya sabuwar kwantiragin shekaru biyu a Crystal Palace.

Chamakh, mai shekaru 30, ya je kulob din ne daga Arsenal bayan da kwantiraginsa ta kare a kakar bara - sai dai ya shafe shekara daya a matsayin aro a Crystal Palace.

Bayan ya fara da kafar hagu, zuwan koci Tony Pulis ya taimaka wa Chamakh inda ya kare kakar da kwallaye shida.

A yanzu Chamakh zai tafi zuwa Austria domin hadewa da sauran 'yan wasan Palace a atisayinsu domin shiryawa kakar wasanni ta bana.