Dan Egypt Ahmed Fathi zai je Arsenal

Ahmed Fathi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ahmed Fathi ya bugawa Egypt kwallo sau 101

Dan wasan Egypt Ahmed Fathi zai je Arsenal domin yin gwaji, kamar yadda kulob dinsa na Al Ahly suka bayyana.

Al Ahly sun sanar a shafinsu na Facebook, cewa Fathi na tafiya Ingila ranar Juma'a "da fatan sanya hannu kan kwantiragi idan yayi nasara".

Dan kwallon mai shekaru 29 ya taba taka leda na wani dan lokaci a gasar Premier tare da Sheffield a shekara ta 2007.

Ya shafe watanni shida a matsayin aro a Hull City a Championship a kakar 2012/13.

Fathi, wanda ya bugawa Egypt kwallo sau 101, kulob din Nottingham Forest ma sun taya shi a watan Janairu.