Jamus sun nemi goyon bayan Brazil

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamus za ta kara da Argentina a wasan karshe ranar Lahadi

Jamus sun yi kira ga al'ummar Brazil da su goyi bayansu a wasan karshen da za su fafata da Argentina ranar Lahadi.

Tawagar ta Joachim Low sun lallasa Brazil da ci 7-1 a wasan kusa da na karshe amma sun yabawa yadda halayyar magoya bayan Brazil din bayan an tashi.

"Dukkanmu muna fatan samun goyon bayan jama'ar Brazil," a cewar dan wasan bayan Jamus Benedikt Howedes.

"Ina ganin 'yan Brazil sun yi mana kara ganin yadda suka yi murnar nasarar da muka samu."

Karin bayani