Holland ta casa Brazil 3-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An zura wa Brazil kwallaye 14, da hakan ya sa ta zama kasar da aka fi ci a gasar

Holland ta samu matsayi na uku a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ake yi a Brazil bayan ta lallasa Brazil da ci 3-0.

van Persie ne ya fara jeafa kwallo a ragar Brazil da bugun fanareti minti uku da shiga fili.

A minti na 16 ne kuma sai Blind ya ci ta biyu, kafin kuma Georginio Wijnaldum ya kara ta uku ana shirin tashi bayan minti 90.

Wannan shi ne karon farko da Holland ta zama ta uku a gasar cin kofin duniya.

A ranar Lahadi ne kuma za a samu kasar da za ta kasance ta daya da ta biyu, a wasan karshe tsakanin Jamus da Argentina.

Karin bayani