Rodriguez ya ci Goolden Boot

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rodriguez ya dauki kofin lig uku a jere da Porto yana shekara 21

Dan wasan Colombia James Rodriguez ya ci kyautar takalmin zinare (Golden Boot),a matsayin wanda ya fi cin kwallo a gasar kofin duniya ta Brazil.

Dan wasan na gaba mai shekaru 23 da ke wasa a kungiyar Monaco, ya ci kwallaye shida a wasanni biyar.

inda kasarsa ta kai wasan dab da na kusa da karshe kafin Brazil ta fitar da su da ci 2-1.

Thomas Muller na Jamus wanda kasarsa ta dauki kofin shi ne ya zo na biyu da kwallaye biyar.

Lionel Messi, wanda ya samu kyautar kwallon zinare (Golden Ball), a matsayin zakaran dan wasan gasar shi ne na uku.

Shi kuwa mai tsaron gidan Jamus, Manuel Neuer mai shekaru 28, ya samu kyautar safar hannu ta zinare (Golden Glove), a matsayin golan da yafi kwanne a gasar.

Paul Pogba na Faransa mai shekaru 21 shi ne zakaran matashin dan wasa na gasar ta kofin duniyar na 2014.