Jamus ta dauki Kofin duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Karon farko da Jamus ta dauki kofin duniya a matsayin dunkulalliyar kasa

Jamus ta doke Argentina a wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, abinda ya bata nasarar dau kar kofin.

Dan wasan nan Mario Gotze ne ya zura kwallo a ragar Argentina bayan da aka dawo zagaye na biyu na karin lokaci.

An dai shafe mintuna casa'in babu inda aka ci abinda ya sa aka shiga karin lokaci na mintuna talatin.

Jamus dai rabon ta da ta ci gasar kofin duniya tun 1990 lokacin da ta doke Argentina a Rome.

Karin bayani