Argentina da Jamus za su ja zare

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Golan Argentina Romero da Neuer na Jamus

Duniya za ta zuba idanu a filin wasa na Maracana da ke birnin Rio na Brazil inda kasar Argentina za ta fafata da Jamus a wasan karshe na cin kofin duniya.

Gasa ce da ta tara tawagar 'yan wasan kasashe 32 wadanda suka shafe dubban mila-milai tsakanin birane 12 da suke karbar bakuncin Gasar, kama daga Manaus zuwa birnin Gaucho da ke Porto Alegre.

Amma dai a karshe sauran tawagar 'yan wasan sun ja baya sai guda biyu inda a cikinsu daya zata lashe kyautar.

Wannan shi ne karo na uku da kasashen biyu ke haduwa a wasan karshe na cin kofin duniya, inda a baya sun hadu a 1986 da 1990 lokacin ana kiran tawagar Jamus da 'West Jamus' ta kuma yi nasara sau daya tal kan Argentina.

Jamus ta fara wasan da kafar dama biyo bayan jefawa Brazil kwallaye 7 a raga, amma tawagar ta fara yanke kauna inda ta ke kokarin rike matsayin da su ke da shi na da'a kamar yadda aka gani a zagayen farko na wasan su da Algeria.

Har yanzu dai Argentina ba a gwada karfin ta sosai ba, ganin yadda ta fito a rukuni kasashen da ba su da karfi, suka kuma gamu da 'yan dagaji irin kasar Switzerland da Belgium wadda a galabaice ta ke, kafin su makure Netherland a bugun finariti wanda in ban don haka ba, watakila da labari ya sha banban.

Amma dukkannin kasashen biyu na da magoya baya a Rio.

Jamus na iya zama kasa ta farko da za ta ci kofin duniyar a yankin kudancin Amirka tare da zama kasar da ta fi kowacce cin kwallaye a tarihin Gasar cin kofi duniya ta irin ruwan kwallayen da suka zura a ragar Brazil.

Shekaru 28 daidai rabon Argentina da daukar kofin, bayan da suka yi nasara a kan Jamus da ci 3-2, amma tun daga lokacin ba su sake kai wa wasan karshe a Gasar ba tun 1990. Samun nasara a Brazil hakika abun farin ciki ne.

Tun da aka fara Gasar, Argentina ta alaqan ta nasarar ta kan shaharran dan wasanta Lionel Messi. Yawan kwallayensa sun tabbatar da kokarinsa a tsakanin rukunin da suka fito, amma nasarar daukan kofin a wasan karshe ita ce zata ba shi damar fitowa karkashin inuwar Maradona.

Sai dai Jamus na da shaharren dan wasanta Miroslav Klose wanda ya kafa tarihi a gasar cin kofin duniya a wasansu na kusa da karshe da Brazil, yayin da Thomas Muller ke bin dan wasan Columbia James Rodriguez a neman kyautar 'Golden Boot'.

A kalla ana sa ran kimanin 'yan kallo 75,000 za su halarci wasan, sannan akwai kuma wani abin sha'awa wajen ganin kasar da magoya bayan Brazil za su marawa baya.

Ko za su bi bayan Amirka ta kudu ne su mara wa Argentina baya, ko tunanin ajiye kofin a Buenos Aires zai sa su su goyi bayan Jamus wacce ta koya musu darasi a fagen wasan kwallo kafa?

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba