Liverpool na daf da sayen Markovic

Lazar Markovic Hakkin mallakar hoto
Image caption Dan kwallo na hudu kenan da Liverpool za ta dauka.

Kulob din Liverpool na tattaunawa da Benfica domin musayar dan wasanta Lazar Markovic.

Markovic dan kwallon Serbiya mai shekaru 20, an yi hasashen darajarsa zata kai fam miliyon 20 da ake sa ran kammala cinikinsa nan da awanni 24.

Haka kuma Liverpool na jiran amincewar Divock Origi ya yanke hukuncin ko zai koma kulob din, bayan da Lille ta cimma yarje-jeniya da Liverpool kan cinikin dan wasan.

Dan wasan Liverpool dake shirin barin kungiyar, shi ne Iago Aspas wanda Sevilla ke zawarcinsa.

Idan Markovic ya isa Liverpool zai zamo dan kwallo na hudu da kulob din ya dauka a bana.