Blatter na mamakin lashe kyautar Messi

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Messi lokacin da ya karbi kyautar gwarzon dan wasa

Shugaban Fifa Sepp Blater yace ya yi mamaki da Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a gasar kofin duniya da aka kammala a Brazil.

Messi, mai shekaru 27 ne ya lashe kyautar duk da dokesu da Jamus ta yi a wasan karshe da ci daya mai ban haushi.

Shi ma tsohon dan kwallon Argentina Diego Maradona yace ba ayi adalci ba a zaben.

Kyautar gwarzon dan wasa da sauran kyautuka a gasar kofin duniya, kwamitin tsare tsare na Fifa ne da masu fashin baki da suka hada da tsohon kocin Liverpool Gerard Houllier suka gudanar da shi.