Tsoro ke hana 'yan Ingila kwallo a wasu kasashe

Ashley cole Hakkin mallakar hoto officilaASRoma
Image caption yakamata 'yan kwallon Ingila su dunga buga wasa a wasu kasashe

Tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea Ashley cole, yace tsoro ne yake hana 'yan kwallon Ingila komawa wata kasar domin buga wasanni.

Cole, mai shekaru 33, ya koma Roma ta kasar Italiya, bayan da kwantiraginsa ta kare da Chelsea a karshen kakar bara.

"Yan wasan Ingila sun fi sakin jiki da buga gasar Premier, saboda haka suna fargabar zuwa wata kasa domin nuna kwarewarsu".

Cikin tawagar 'yan kwallon Ingila da suka buga kofin Duniya da Brazil ta dauki nauyi Fraser Forster golan Celtic shi kadai ne baya wasa a gasar Premier.