Sevilla ta aro Aspas daga Liverpool

Dan wasan Liverpool Iago Aspas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kulub din na Spaniya ka iya sayen dan wasan a shekara mai zuwa zuwa.

Dan wasan Liverpool Iago Aspas ya sanya hannu a kan kwantiragin aro da kungiyar Sevilla har zuwa karshen kakar wasa mai zuwa.

Kulub din na Spaniya ka iya sayen dan wasan mai shekaru 26 a shekara mai zuwa, na tsawon shekaru uku kamar yadda yarjejeniyar ta ce.

Aspos ya koma kungiyar Liverpool daga Celta Vigo a farkon kakar da ta wuce a kan kudi £7m.

Sai dai dan wasan ya buga wasanni 14 ne inda ya ci kwallo daya kacal.

Sai likita ya masa gwaji tare da tabbatar da lafiyarsa kafin kungiyar ta dauke shi.

Kungiyar Liverpool ta amince ta sayarwa Barcelona Luis Suarez a kan kudi £75m, sai dai su na dab da sayen dan wasan Benfica Lazar Markovic a zaman kari a kan tsaffin 'yan Southampton Adam Lallana da Rickie Lambert.

Karin bayani