Liverpool ta kammala cinikin Markovic

Lazar Markovic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallo na hudu da Liverpool ta dauko a bana

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kammala cinikin dan kwallon Serbia Lazar Markovic daka Benfica.

Markovic, mai shekaru 20 shi ne dan wasa na hudu da Liverpool ta dauko a bana.

Tsohon dan kwallon Partizan Belgrade, ya taimakawa Benfica lashe kofin gasar Portugal a bara.

Liverpool ta dauko Rickie Lambert da Adam Lallana daga Southampton da Emre Can daga Bayer Leverkusen.