Nigeria na tsaka mai wuya saboda NFF

Image caption Fifa ta yi fushi saboda gwamnati ta cire Aminu Maigari

Nigeria na cikin hadarin kasa cika wa'adin da Fifa ta gindaya na ranar Talata domin maido da jami'an hukumar kwallon kasar - NFF wandanda ta cire.

Gwamnatin Nigeria na cikin rashin tabbas ne saboda yajin aikin da ma'aikatan shari'a ke yi.

A makon daya gabata ne Fifa ta dakatar da Nigeria daga shiga harkokin kwallon kafa saboda zargin gwamnati na katsalandan a harkar kwallon kasar.

Sai dai gwamnatin ta ce ta cire jami'an NFF ne bisa umurnin wata babbar kotu a jihar Filato.

Idan har Nigeria ba ta maidoda shugabannin NFF, a karkashin jagorancin Aminu Maigari ba, to kasar ba za ta halarcin gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 da ake soma wa a watan Agusta a Canada.

BBC ta fahimci cewar yajin aikin ma'aikatan shari'a shi ne babban tarnakin da kasar ke fuskanta a kokarin maidoda jami'an NFF din.