Fifa ta kara dagawa Nigeria kafa

Nigeria
Image caption Fifa ta sake baiwa Nigeria damar dawo da mahukuntan kwallon kafar kasar da aka sauke

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta kara tsawaitawa Nigeria, da ta maida korarrun mambobin hukumar kwallon kasar nan da ranar Juma'a.

Fifa ta dakatar da Nigeria daga shiga duk wata sabga data shafi kwallon kafa, sakamakon tsoma bakin gwamnati a harkokin hukumar kwallon kafar kasar.

An cire mahukuntan hukumar kwallon kafar kasar ne bayan da wata kotu ta yanke hukuncin sauke su daga aiki.

An shirya sake sauraren karar, amma yajin aikin ma'aikatan shari'ar kasar ya jawo tsaiko.